<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>176</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Na ta da idona wurin Mai Cetona,
 Wurin Yesu.
 Na bata hanya fa, na faɗa jaraba,
 Sai ka ji roƙona, Mai Cetona.

[V2]
 2) Na faɗi laifina, na faɗi aibina
 Wurin Yesu.
 Zuciyata mai dauɗa, ka iya wankewa.
 Sai ka ji roƙona, Mai Gafara.

[V3]
 3) Shugabance ni dai a wannan duniya,
 Ina addu'a.
 Kwaɗayin zuciyata ya kawo jaraba.
 Ka iya gyartawa, Mai Cetona.

[V4]
 4) A ranar mutuwa, sai ka bishe ni kuwa
 Har Sama can.
 Saboda giciyenka, ina da fansata,
 Nan gaba na yarda in bi Yesu.</lyrics>
<title>Na Ta da Idona Wurin Mai Cetona LW176</title>
</song>